Da duminsa: Kauran Bauchi ya yi sabuwar amarya balarabiya.Hotuna


Legit Hausa

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya auno sabuwar amarya balarabiyar kasar Labnan amma mazauniyar Najeriya. Wannan labarin ya bayyana ne ranar Juma'a inda mai magana da yawun gwamnan, Ladan Salihu, ya ce an daura wannan aure a Masallacin Syriya dake Jihar Legas.


Sabuwar amaryar za ta kasance matar gwamnan ta biyu. Kauran Bauchi ne gwamnan Najeriya na uku wanda ya kara aure jim kadan bayan darewa karagar mulki. Ya bi sahun gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda ya yi aure bayan zabe.

Yace: "Alhamdulillah yau min shaida Fatihar Amaryar Gwamnan Jihar Bauchi Sen Bala A Muhammad a Masallachin Syria dake Ribadu Road a Lagos. Allah ya bada zaman lafiya. Amin."
 

DAGA ISYAKU.COM

 Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post