Cin zarafin Musulmi: Amurka ta haramtawa Janar shiga kasarta tare da hafsoshi 3

Kasar Amurka ta maka wa wani babban Janar Ming Aung Hlaing na sojin kasar Myammar tare da wasu manyan hafsoshi guda uku takunkumin hana shiga kasar Amurka bisa zargin take hakkin bil'adama ta hanyar cin zarafin Musulmin Rohingya.

Takunkumin ya shafi hafsoshin tare da iyalanasu wadanda aka haramtawa shiga kasar Amurka.

Sakataren harkokin cikin gida na Amurka Mike Pompeo ya ce, akwai kwakwakwarar shaidar cewa wadannan hafsoshi na da hannu a cin zarafi da aka yi wa Musulmin Rohingya a 2017.

Gwamnatin kasar Myammar dai ta yi Allah wadai da wannan mataki da Amurka ta dauka, yayin da sojin kasar Myammar suka kira wannan takunkumi rashin adalci.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN