Legit Hausa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dattijai ta amince da nadin Farfesa Habu Galadima a matsayin sabon babban darektan cibiyar horon manyan jami'an gwamnati (NIPSS) da ke Kuru, a Jos, jihar Filato.
Shugaban majalisar dattijai, Dakta Ahmad Lawan, ne ya karanta wasikar da shugaban kasar ya aiko zuwa majalisar yayin zaman ta na ranar Talata.
Buhari ya ce sashe na 8 (5) na dokokin NIPSS ne ya bashi ikon rubuta wasikar da ya aika wa majalisar a ranar 9 ga watan Yuli.
Ya bukaci mambobin majalisar su bashi hadin kai wajen tabbatar da nadin Farfesa Galadima a matsayin shugaban NIPSS ba tare da wata matsala ba.
Shugaban kasar ya hada da takardun Farfesa Galadima da ke dauke da irin karatun da ya yi da kuma gogewarsa a aiki da kuma dukkan wasu bayanai da zasu taimaka wa majalisar wajen tantance shi.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa an haifi Galadima a shekarar 1963 a karamar hukumar Toto da ke jihar Nasarawa.
Yanzu haka Galadima farfesa ne a fannin kimiyyar siyasa a jami'ar Jos, jihar Filato, inda ya yi digirinsa na farko; a shekarar 1987, da na biyu(MSc); a shekarar 1990, da na uku (PhD); a shekarar 2006.
Farfesa Galadima ya rike shugaban sashen karatun kimiyyar siyasa a jami'ar Jos, sannan ya taba aiki da kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) da bankin duniya da wata kungiyar majalisar dinkin duniya (UNDP)
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi