Babban zance! Wani Lauya ya shirya auren kanshi da kanshi a birnin Abuja


Legit Hausa

Wani dan Najeriya ya yanke hukuncin auren kanshi da kanshi inda har ya aikawa 'yan uwa da abokanan arziki katin gayyata na daurin aurensa. Irin auren shin dai ana kiransa da suna 'Sologamy' a turance, inda namiji zai auri kanshi ko kuma ta mace ta auri kanta, kuma hakan shine fitaccen Lauyan na birnin Abuja yake shirinn yi.

Victor wanda yake da shafin Facebook guda biyu daya nashi daya kuma na kasuwancinsa, ya wallafa a kowanne shafi cewa ya gama shiri tsaf domin aurar kanshi. Abokanan shi da yawa sun fara taya shi murna inda suke aika masa da sako.

Lauyan wanda yayi suna a shafin Facebook wajen kokarin ganin ya jawo hankalin mutane sun fada soyayyar kansu, ya kuma wallafa wani katin gayyatarsa, inda ya ya ce: "Soyayyace! Ina gayyatarku daurin aurena, wanda zan auri kaina da kaina." Wannan lamari dai kamar shine na farko da ya fara faruwa a Najeriya, amma a wasu kasashe na duniya wannan ba bakon abu bane.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post