Ba jira: Shugaba Buhari zai rantsar da sababbin ministo a ranar Laraba

Legit Hausa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rantsar da sabbin ministocinsa a ranar Laraba, 31 ga watan Yuli bayan kammala aikin tantancesu da majalisar dattawan Najeriya ta yi a ranar Talata, 30 ga watan Yuli.
Rahoton jaridar Guardin ne ya bayyana haka, inda tace fadar shugaban kasa ta kammala shirin kwarya kwaryan taron da za’a gudanar wajen karbar rantsuwar da sabbin ministocin da zasu yi daga wajen shugaban kasa Buhari a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a gobe.
A ranar Talata, 30 ga wata ne majalisar ta kammala tantance sunayen mutane 43 da shugaban kasa ya aika mata don nadasu mukamin minista, inda majalisar ta amince da dukkanin mutanen don samun mukamin minista a sabuwar gwamnatin Buhari.
Sai dai har yanzu yan Najeriya na cikin duhu game da ma’aikatun da shugaban kasa zai tura sabbin ministocin, amma majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu daga cikin tsofaffin ministocin da Buhari ya sake nadawa zasu koma tsofaffin ministocinsu, daga cikinsu akwai:
Zainab Ahmed ma’aikatar kudi, Babatunde Fashola ma’aikatar ayyuka, gidaje da lantarki, Geoffrey Onyeama ma’aikatar kasashen waje, Rotimi Amaechi ma’aikatar sufuri da Lai Mohammed ma’aikatar watsa labarai.
A hannu guda kuma shugaban kasa Buhari ya sha suka game da karancin mata a cikin sabbin ministocin nasa, da suka hada da Sharon Ikeazor, Gbemisola Saraki, Ramatu Tijjani-Aliyu, Sadiya Farouk, Mariam Katagun, Pauline Tallen da Zainab Ahmed.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post