Legit Hausa
Friday Okeke, wani mutum da aka kama da laifin aikata luwadi
da kananan yara, ya shaida wa 'yan sanda cewa yafi jin dadin lalata da yara
maza masu karancin shekaru a kan mata. Jami'an rundunar 'yan sanda sun ce sun
kama Okeke, dan kasuwa, dumu-dumu ya na lalata da yara biyu a cikin shagonsa da
ke Ebute-Ero a jihar Legas.
Kazalika sun bayyana cewa ya shaida musu da bakinsa cewar ya
na kyamar mata, musamman kazamai daga cikinsu. A cewar 'yan sandan, Okeke ya
shaida musu cewa mata sun bata kansu da kyale-kyale da salon shiga irin na
Amurkawa yayin da maza suka zabi zama a yadda halittarsu ta ke. Okeke ya ce,
"na kan ji jama'a na cewa wai masu saduwa da maza na yin hakan ne saboda
dalilan tsafi, amma, ni a wuri na, don jin dadi ne, na fi jin dadin kwanciya da
yara maza a kan mata, duk da na yi nadamar saka yara a cikin harkar
luwadi."
Okeke ya bayyana cewa yara da yawa na shiga harkar luwadi ta
hannun mutanen yaran da suka amince tare da sakin jiki da su. Kakakin rundunar
'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya shaida wa manema labarai cewa sun kama
Okeke, mazaunin gida mai lamba 23 a kan titi Kose, bayan samun korafi daga
wurin iyayen wasu yara.
Elkana ya ce iyayen yaran sun shigar da korafin zargin Okeke
da yaudarar yaransu (da aka boye sunayensu), masu shekaru 12 da 9, zuwa
shagonsa tare da saduwa da su ta dubura. Kakakin ya kara da cewa an dauki yaran
zuwa babban asibitin jihar Legas domin gudanar da bincike a kan lafiyarsu,
yayin da wata rundunar 'yan sanda ta musamman karkashin DPO na ofishin Ebute
Ero ta kama Okeke.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi