An yi mun barazana ne yasa dole nasa hannu a sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 - Mohammed Tata

Legit Hausa
Mista Mohammed Tata, wanda shine mutum na biyar da Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP suka gayyato a matsayin shaidan su a kotun shari’ar zaben shugaban kasa, ya shaidawa kotu cewar; tilasta shi aka yi ya sanya hannu a sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 a jihar Jigawa.
“An yi mun barazana gami da tsoratar da ni domin in sa hannu a sakamakon zaben shugaban kasa, sannan aka gaya mun cewar idan ban sanya hannu ba za’a cire suna na a cikin ma’aikatan N-power.” Inji Mohammed Tata.
Da aka yi masa tambaya, ko bai aminta cewa shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC sun sami kuri’a 700 ba ne a akwatin sa, Mohammed yace “Ai babu alkalumman zabe domin ba’a ma yi zabe a wajen ba.”
Tata, ya kara da cewar “Ni musulmi ne, na yi imani da kaddara kuma duk abinda yaso ya faru shi zai faru, ko PDP ta yi nasara ko APC tayi nasara ba ni da matsala da wannan, abinda nake bukata kawai shine ayi shari’ar adalci a kasa ta.”
“Ban damu da nasarar jam’iyya ko faduwar ta ba, amma dai ban ji dadin abinda ya faru ba.” Cewar Mohammed Tata.
Da aka sake tambayar Mohammed Tata, ko an bashi kwafin sakamakon zaben, sai yace “A’a ba’a bani ba saboda rigima babu zaman lafiya a wajen.”
“Na bi duk hanyoyin da suka dace wajen kai rahoton abubuwan da suka faru na barazanar da aka yi mun, amma ba’a hukunta wadanda suka aikata laifin ba.”
“Ban bayyana sunansu ba a cikin bayanai na saboda dalili na tsaro, anma dai har yanzu ina aiki da N-Power saboda na sanya hannu a sakamakon zaben, inda ban saka hannu ba da yanzu sun kore ni daga aiki na.” A cewar Mista Mohamed Tata shaidan Atiku da PDP a gaban kotun shari’a.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN