An yanke wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa kafa daya sakamakon rashin lafiya (Hotuna)

Legit HausaAn yanke wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Sani Idris, daya daga cikin kafafunsa sakamakon rashin lafiyar da ke damunsa. Jarumi, Sani Idris, da aka fi sani da 'Moda' ya dade ya na kwance a asibiti, karkashin kulawar likitoci, bayan ciwon da ke damunsa ya yi tsanani.

Moda na fama da matsanancin ciwon sukari (Diabetes), kuma an kwatar da shi a asibiti tun cikin shekarar da ta gabata. Halin da jarumin ke ciki ne suka jawo wassu kafafen yada labarai da ma'abota rubuta a dandalin sada zumunta suka fara jita-jitar cewa Moda ya mutu a cikin watan Mayu na shekarar 2018, kafin daga bisani ya fito ya bayya cewa yana nan da ransa.

Tun bayan kwantar da Moda, manyan jaruman fina-finan Hausa da suka hada da Ali Nuhu da manyan darektoci irinsu Falalu Dorayi ke zarya zuwa asibitin da aka kwantar da shi domin duba lafiyarsa.Moda na daga cikin jaruman fina-finan Hausa da suka dade an dama wa da su a masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood). Jarumin ya samo sunan 'Moda' ne sakamakon rawar da ya taka a wani tsohon shirin wasan Hausa mai suna 'Wasila'.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN