An sake kama wani malamin islamiyya bayan ya yi wa dalibarshi fyade a cikin wani otel


Legit Hausa


Rahotanni sun kawo cewa ana zargin wani malamin addini a jihar Osun mai suna, Habeebulah Abdulrahman wanda aka fi sani da Al-Edewy da yiwa dalibarsa mai shekara 16 fyade. Da yake martani, Abdulrahman ya bayyana wa majiyarmu ta Premium Times cewa yarinyar matarsa ce kuma cewa yana da ikon Tarawa da ita. Anhaifi yarinyar a sjekarar 2003, ta kuma rasa mahaifinta tun tana yar karama amma sai tana zama da mahaifiyarta a Ede, wani gari a jihar Osun.

Bata dade da kammala makarantar karamar sakandare ba Bincike ya nuna cewa malamin a watan Janairu ya gayyaci yarinyar domin ta fara zuwa makarantar Islamiyarsa wanda bai da nisa da gidansu, domin koyon karatun Al-Qur’ani. Sai yarinyar ta fara da amincewar mahaifiyarta.

Sai dai kuma bayan dan lokaci kadan sai malamin ya nemi auranta yarinyar ta ki amincewa amma Abdulrahman ya ci gaba da nace mata har said a yayi mata fyade. Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa yana ta bai wa yarinyar kyaututtuka da nufin jan hankalinta domin ta aure shi, amma da aka tunkare shi sai yayi ikirarin cewa yana tallafa mata ne domin ta kasance marainiya.

Yadda abun ya faru: A ranar 18 ga watan Afrilu, malamin yayi tafiya zuwa Ilaro da ke jihar Ogun domin halartan wani taron wa’azi tare da yarinyar da kuma wasu dalibai maza biyu Yayinda aka yiwa daliban maza biyu masauki a waje guda, Mista Abdulrahman ya sauka daki daya dashi da yarinyar yayi kokarin Tarawa da ita amma ta ki, sannan ta ja hankalin masu otel din, inji ta Yarinyar tayi ikirarin cewa yayi mata fyade a wannan ranar.

A hanyarsu ta dawowa jihar Osun, malamin ya ziyarci yan uwansa a Abeokuta, inda ya sake yiwa matashiyar fyade. A cewar yarinyar, a Abeokuta, ya tara da ita ta karfin tuwo a baya idon daliban maza biuyu da yan uwansa A halin da ake ciki bayan fyaden, yarinyar ta daina halartan makarantar Islamiyyan sannan iyayenta suka yi shiru kan lamarin har sai da dan uwanta da ke zama a wajen Osun ya samu labara a lokacin da ya ziyarci Ede a watan Yuni.

A cewar mahaifiyar yarinyar, Misis Ibrahim, malamin ya fara duba kokarin yarinyar a makaranta, wanda hakan yasa take ganin kawai yana tausayin iyalin ne. Sai da suka sakankance dashi ya aikata masu ta’asa, ta kuma nemi Allah ya saka musu.

A nashi bangaren malamin yayi ikirarin cewa an daura masu aure daidai da koyarwar addini, ana gobe za su yi tafiya amma ba wai fyade yayi bata ba. “Matata ce ba wai daliba kawai ba. Ta yi rashin hankali ne kuma na fada ma iyayenta cewa bana muradinta kuma iyayen nata na son tursasa ni aurenta. Abunda tayi, bana tunanin akwai wanda zai yarda da hakan. Ta je gidan wani mutum tsawon kwanaki biyu. “Bayan kwana 15, sai na ga hotunan. Na je ga yan uwanta da mahaifiyarta na nuna masu hotunan.

A lokacin ne na bayyana cewa bana muradinta kuma. Tun lokacin suke ta kullamun sharri don na aure ta." Da aka tambaye shi ko akwai takardu ko hotuna da za su tabbatar da ikirarin cewa sun yi aure, bai gabatar da kowane ba amma ya bayyana cewa yan uwan yarinyar maza su biyu da abokinsa sun shedi auran.

Sai dai yan uwan yarinyar sun karyata batun masaniya kan auren, inda suka bayyana cewa haduwar da suka yi don tattauna batun kin amincewa da auren malamin da yarinyar tayi ne. A lokacin da aka tuntubi yan sandan jihar Osun, wanda ke rike da laamarin, sun bayyana cewa hukumar tsaro na gudanar da bincike na musamman sannan cewa za su gano bakin zaren.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN