An kama mutum 6 da suka yi wa matar aure fyade a garin Warra jihar Kebbi

Rundunar yansandan jihar Kebbi ta kama mutane shida bisa zargin yi ma wata matar aure fyade tare da yi ma wasu yan mata guda biyu fyade a garin Warra da ke karamar hukumar Ngaski.
Kwamishinan yansandan jihar Kebbi Alh. Garba Danjuma ne ya shaida wa manema labarai haka a garin Birnin kebbi ranar Laraba.
Ya kara da cewa yansanda sun kama wani mai suna Usman Alhaji Lawal tare da wasu mutum biyu bayan sun kai ma wata mata mai suna Safiya Audi hari da adduna suka kwace N92.250 a hannunta kuma suka keta mutuncin aurenta.
Hakazalika Garba Danjuma ya ce, ranar 10 ga watan Yuni, rundunarsa ta kama Badamasi Mamuda mai shekaru 25, Yahuza Aliyu shekaru 23 da Anas Abubakar mai shekaru 20, dukkansu yan garin Warra. An kama su ne bayan sun yi ma wasu yan mata masu suna Fatima Ibrahim mai shekaru 13 da Shafa’atu Sani, mai shekaru 13 fyade.
Kwamishinan ya ce an kama mutanen da awaki 29 da shanaye 2, kuma ana zargin suna cikin gungun masu satar shanaye daga jamhuriyar Nijar wadanda ke shigowa ta karamar hukumar Arewa dandi. Ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifinsu.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN