Legit Hausa
An gano babban sojan kasar Zimbabwe da ke yi wa Amai
Auxillia Mnangagwa, uwargidan shugaban kasar Zimbabwe leken asiri tare da
shirin kifar da gwamnatin shugaba Emerson Mnangagwa. Babban hafsan sojin,
laftanal kanal Samson Murombo, kwamanda ne a rundunar sojoji da 1 da ke tsaron
shugaban kasa.
TALLA: Domin cire makulli ko sikiritin wayarka ko FLASHIN ko gyara wayarka a jihar Kebbi, ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50, Taushi Plaza yamma da gidan Wairin Gwandu, kan Titin Ahmadu Bello, Birnin kebbi.
Wani dan kasar Zimbabwe ne ya fara tona asirin kanal Murombo
a shafinsa na Tuwita kafin daga bisani tsohon ministan ilimi a kasar, Jonathan
Moyo, ya yada wani faifan sautin muryar matar shugaban kasa, Auxillia
Mnangagwa, ta na babatu a kan shirin wani soja na yi wa mijinta, shugaba
Emmerson Mnangagwa, juyin mulki. Kazalika ta koka a kan yadda sojan ke yi mata
leken aisiri.
Ana zargin kanal Murombo da hada baki da da Mhlanga da
Manjoro domin yi wa Mnangagwa juyin mulki, kamar yadda uwargidan shugaban kasa
ta yi zargi.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi