Allah Ya tona asirin matashin daya shahara wajen satar wayoyin salula a Masallatai

Legit Hausa
Dubun wani matashi daya shahara wajen satar wayoyin salulan jama’a a cikin Masallatai a jahar Legas ta cika, a ranar Litinin 8 ga watan Yuli ne aka gurfanar da wannan matashi mai suna Wasiu Sosun gaban kotun majistri dake Legas.
Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa an gurfanar da matashin ne akan tuhumarsa da laifin sata da kuma daukan abinda ba nasa ba a gaban kotun majistri dake unguwar Tinubu na jahar Legas.
Dansanda ma shigar da kara, Inspekta Ben Ekundayo ya shaida ma kotun cewa Wasiu dan shekara 21 ya aikata wannan laifi ne a ranar 28 ga watan Yuni a masallacin Kuti dake tsibirin jahar Legas.
Dansandan yace a wannan rana, Wasiu ya shiga cikin Masallacin ne inda ya yi kasake kamar yana Sallah, amma ashe ba sallah yake yi ba, kwantan bauna yake yi yana shirin cutar bayin Allah masu ibada.
“Sai da ya gama kallon masallatan tsaf, sai kawai ya wawuri wayoyin wasu masallata guda biyu, da darajarsu ta kai N8,000, kuma ya fita masallacin da gudu, don kuwa hatta jama’an da suka bi shi da nufin kamashi basu daman kama shi ba.” Inji Dansandan.
Dansandan yace laifin da Wasiu ya aikata ya saba ma sashi na 287 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Legas na shekarar 2015, kuma sashin ya tanadar da hukuncin zaman shekara uku a gidan yari ga duk wanda aka kama da laifin.
Shima Wasiu na take ya amsa laifinsa ba tare da ya baiwa sharia wahalaba, don haka bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, sai Alkalin kotun, mai shari A.M Olumide-Fusika ya bada umarnin garkame Wasiu a gidan Yari har zuwa ranar 18 ga watan Yuli kafin ya yanke masa hukunci.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN