Abba Vs Ganduje: Kotu ta hana wani dan Kwankwasiyya bayar da shaida


Legit Hausa


Kotun sauraron korafin zaben gwamnan jihar Kano da ke zaman ta a unguwar Bompai ta ki amincewa wani shaidar masu kara, Muhammad Buhari Sule, ya yi bayani a gaban ta yayin zaman kotun na ranar Litinin.

Kin amincewar kotun ya biyo bayan korafin da lauyan INEC, Dayo Adedeji, ya yi yayin da aka kira mutumin a matsayin shaida na farko da masu kara suka kira domin ya fara gabatar da jawabi a gaban kotun a karar da jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna a Kano, Abba Kabir Yusuf, suka shigar.

Lauya Adedeji ya yi korafi ne a kan sunan shaidar da aka kira a gaban kotun, inda ya ce sunansa bai yi daidai da sunan da ke cikin takardar jerin sunayen shaidun da masu kara suka gabatar a gaban kotun ba. "Mai girma, mai shari'a, abinda muke da shi a rubuce a sunan shaidar shine 'MD', amma kuma shi shaidar ya bayyana cewa sunansa Muhammad Buhari Sule, wanda hakan ya saba da abinda masu kara suka gabatar kuma suka rantse a kan sa.

"Babu yadda za ai MD ya zama Muhammad Buhari Sule koda kuwa an dauki harufan farkon sunansa ne, a saboda haka ina kira ga wannan kotu mai albarka da ta hana wannan shaida yin magana," a cewar lauya Adedeji. Da ya ke kalubalantar gabatar da shaidar, M. M Duru, lauyan gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce doka ta yarda a boye sunan shaida, amma tunda shi shaidar da kansa ya bayyana sunansa, ba zai ci moriyar dokar da ta amince da boye sunan shaida ba.

Sai dai, a martaninsa, lauyan jam'iyyar PDP, Eyitayo Fatogun, ya ce bisa dokar kotun sauraron korafin zabe ta shekarar 2011, ana boye sunan shaida ne domin bashi kariya. A nata hukuncin, babbar alkaliyar kotun, Jastis Halima S. Muhammad, ta ce tunda masu kara na yin amfani da harufan farko na suna domin sakaya sunan shaidunsu, ta amince cewa 'MD' bai yi daidai da sunan Muhammad Buhari Sule ba, a saboda haka kotu ba zata karbi shaidarsa ba.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN