Zamfara: Jam’iyyar APC na shirin sake kalubalantar wasu kujerun gwamnati

Legit Hausa
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Zamfara tace ta shirya kalubalantar wasu kujerun mukamai wanda a yanzu jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ce ke kai a jihar.
Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Lawali Liman, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai wanda ya gudana a sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau a ranar Laraba, 26 ga watan Yuni.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), ta ruwaito cewa dukkanin matsayin gwamnati a zaben 2019 a jihar na a hannun APC ne har sai bayan da kotun koli ta zartar da hukuncin soke ta.
NAN ta kuma ruwaito cewa kotun ta yanke hukunci ne akan rashin bin ka’ida daga zaben fidda gwani na jam’iyyar kafin zabukan kasa sannan ta kaddamar da jam’iyyar da ta zo ta biyu a matsayin wacce ta lashe zaben.
“Mun yi wata ganawa kwanan nan da Shugaban jam’iyyar na kasa a Abuja wanda ya sanar mani da cewa jam’iyyarmu na da damar kalubalantar matakin da INEC ta dauka bayan hukuncin kotun koli da ta soke zabenmu a jihar.
“Tunda karar da aka shigar kotu na da nasaba ne da rashin bin ka’ida a zaben fidda gwani, muna da yan takara 13 a majalisar dokokin jiha, uku a majalisar dattawa sannan biyu a majalisar wakilai.”
Wadannan mutane ne da suka yi takara ba tare da abokin hamayya ba don haka hukuncin bai shafe su ba.
Don haka Liman yace APC na sake duba cikin lamarin da nufin neman gyara.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN