Zaben 2019: Atiku ya fadi wani tuggu da fadar shugaban kasa ta kulla a Kotun daukaka kara


Legit Hausa

A yayin ci gaba da kalubalantar sakamakon babban zaben kasa na 2019, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gano wani bakin tuggu da fadar shugaban kasa ke kullawa domin cin galaba a kansa a gaban kotun daukaka kara. 

Atiku da kungiyar sa ta kwararrun lauyoyi na ci gaba da zargin fadar shugaban kasa da kawo jinkirin fara sauraron karar sa ta kalubalantar sakamakon zaben kasa domin cimma manufa ta watsi da karar sa. Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, ya shigar da koken sa a gaban shugabar kotun daukaka kara, Jastis Zainab Bulkachuwa, kan kawo jinkiri gabanin fara sauraron karar sa ta kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu. 

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya shigar da korafin sa cikin wata rubutacciyar wasika ta ranar 31 ga watan Mayun 2019 da sanadin daya daga cikin lauyoyin sa, Silas Joseph Onu, da ya ce hakan na zuwa ne da umurnin jagoran kungiyar su ta lauyoyi, Levi Uzokwu. Ko shakka babu an samu jinkirin ci gaba da shirye-shiryen fara sauraron karar Atiku ta kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa yayin da babbar Alkaliya mai shari'a, Zainab Bulkachuwa ta zame hannu ta daga shari'ar.

Legit.ng ta fahimci cewa, domin tsarkake kanta daga tantamar nuna wariya ko kuma rashin gaskiya, Jastis Bulkachuwa ta zame hannun ta kwanaki 11 da suka gabata biyo bayan nasarar mai gidanta ta lashe kujerar Sanatan shiyyar Bauchi ta Arewa a karkashin jam'iyya mai ci ta APC.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN