Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa sabon gwamnan Zamfara wuta


Legit Hausa

A ranar Lahadi, wasu yan bindiga sun budewa motar sabon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, wuta yayinda yake hanyarsa na jajintawa wadanda suka rasa yan uwansu a wani hari da aka kai karamar hukumar Gusau, Premium Times ta bada rahoto. Masu Idanuwan shaida sun bayyana cewa an budewa motar gwamnan wuta ne da yammacin Lahadi a hanyar garin Lilo. 

Majiya ya bayyana cewa Yayinda suka kai harin, yan bindigan sun yi amfani da damar tsayin ciyayi inda suka bude masa wuta. Ya kara da cewa zuwa yanzu ba'a san yawan wadanda aka rasa ko suka jikkata ba, saboda masu tsaron gwamnan sun yi batakashi da yan bindigan. 

A rahoton da muka kawo da saifyar yau, mai magana da yawun Sabon gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyaa cewa gwamnan ya jagoranci ayarin jami’an rundunonin tsaro inda suka fantsama cikin dazukan kauyen Wonaka dake garin Gusau da nufin farautar miyagun yan bindiga da suka addabi al’ummar yankin. 

Kaakakin, Yusuf Idris ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni, inda yace gwamnan ya samu rakiyar mataimakin gwamnan jahar, Mahadi Aliyu Gusau, da sauran kwamandojin rundunar tsaro, inda suka fatattaki yan bindigan. 

A ranar Asabar, Akalla mutane 8 sun rasa rayukansu yayinda 18 suka jikkata harin da aka kai garin Lilo. Har ilau, jihar Zamfara da wasu jihohi basu gushe suna fuskantar barazana daga wajen yan bindiga ba
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN