Legit Hausa
Bayan ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar
Alhamis, 6 ga watan Yuni, Sanata Danjuma Goje ya janye daga tseren takarar
kujerar Shugaban majalisar dattawa. A yanzu dai Goje ya jadadda goyon bayansa
ga Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan domin darewa
kujerar.
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ne ya bayyana
hakan bayan ganawr sirri da suka yi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar
Shugaban kasa da ke Abuja. Gwamna El-Rufai ya kasace tare da Sanata awan,
Sanata Goje, da kuma babban mai ba Shugaban kasa shawara akan harkokin
majalisar dokoki, Sanata Ita Enang a yayinda yake jawabi ga manema labarai na
fadar Shugaban kasa.
Yan majalisar dokoki kasar za su gudar da zabe domin maye
gurbin Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da wani a ranar 11 ga watan
Yuni. Tun da fari dai shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun
nuna goyon bayansu ga Lawan a matsayin wanda suke so ya zama Shugaban majalisar
dattawan.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi