Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya bayyana abubuwan da gwamnatinsa za ta bawa muhimmanci a wannan zangon

Legit Hausa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai cinye shekaru hudun da zai yi yana aiki da kananan hukumomi domin tabbatar da cewa kowanne yaro a kasar nan ya shiga makaranta.
A cewar Buhari wanda ya bayyana haka a shafinsa na Twitter yau Asabar 28 ga watan Yuni, ya kara da cewa gwamnatin tarayya zata ba wa malaman makarantu kayan aiki wadatattu wanda za su ishe su gabatar da koyarwar su yadda ya kamata.
Ga abinda shugaban kasar ya rubuta:
"Za mu cinye shekaru hudun da zamu yi muna aiki da jihohi da kananan hukumomi domin tabbatar da cewa babu wani yaro da ya zauna a gida baya zuwa makaranta; kuma zamu yi kokari mu wadata makarantu da kayan aiki na koyarwa, wadanda zasu ishe su gabatar da ayyukansu yadda ya kamata."
Idan ba a manta ba jiya Juma'a ne shugaban kasar ya bayyana cewa cikin watan Yuli da zamu shiga zai fitar da sunanyen 'yan majalisarsa, wadanda idan kowanne dan Najeriya yake kai domin ganin irin zubin da shugaban kasar zai yi a wannan karon.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN