Yanzu Yanzu: Lawan ya rantsar da Okorocha a matsayin Sanata


Legit Hausa

Sabon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya rantsar da tsohon gwamnan jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha a matsayin Sanata mai wakiltan Imo ta yamma a majalisar dokokin tarayya, a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni.

Magatakardar majalisar dattawa, Nelson Ayewoh, ne ya gudanar da taron rantsarwar bayan Okorocha ya sanya hannu a takardun da ya kamata. Da farko an janye takardar shaidar cin zabe na tsohon gwamnan bayan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tace jami’inta ya sanar da sakamakon zaben ne a karkashin matsin lamba bayan zaben sanata wanda aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

A ranar rantsar da majalisar dattawa ta tara, Mista Okorocha ya halarci wajen taron da safe amma ba a rantsar dashi ba bayan hukumar majalisar sun ki tantance shi. Hukumar INEC ta dai ki bashi takardar shaidar cin zabe duk da cewar wata kotun tarayya ta umurce ta da ta aikata hakan. Sai dai kuma daga bisani a ranar Talata, INEC ta yanke shawarar baa Okorocha takardar cin zaben nasa, amma bisa cewa za ta daukaka kara akan hukuncin kotun.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN