Yanzu-yanzu: Kotun Koli ta kwace kujeran sanata APC, David Umaru


Legit Hausa

Labarin da ke shigowa daga kotun kolin Najeriya da duminsa na nuna cewa kotun a yau Juma'a, 14 ga Yunin 2019 ta kwace kujeran sanatan APC mai wakiltan jihar Neja ta gabas, David Umaru.

Ta alanta Mohammad Sani Musa matsayin zakaran zaben. Kotun kolin ta yi watsi da shari'ar kotun daukaka kara na ranar 8 ga Afrilu, 2019 wacce ta baiwa David Umaru, nasarar cin zaben fidda gwanin jam'iyyar a jihar Neja.

Kwamitin alkalai biyar da suka zauna kan al'amarin karkashin jagorancin Alkali Ibrahim Muhammad, sun yi ittifakin cewa jawaban lauyan Mohammad Sani, Wole Olanipekun, gaskiya ne kuma lallai shi yayi nasara a zaben fidda gwani. Saboda haka, ta tabbatar da shari'ar da Alkaliyar babban kotun tarayya dake Abuja, Folashe Giwa-Ogunbanjo, na cewa Musa ne sahihin dan takarar jam'iyyar APC a zaben.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN