Legit Hausa
Kotun shari'ar zabe shugaban kasa ta yi watsi da bukatar
jam'iyyar Peoples Democratic (PDP) da dan takararta, Atiku Abubakar, na duba
na'urar hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC. A hukuncin,
kwamitin alkalai biyar sun yi ittifakin cewa ba zai yiwu a amsa bukatar PDP ba
saboda an kai ruwa rana kan shin hukumar INEC ta yi amfani da yanar gizo wajen
tattara sakamakon zaben shugaban kasa.
Channels TV ta bada rahoton cewa alkalan sun bayyana cewa ba
zai yiwu sun sanya baki cikin al'amarin ba a wannan lokaci. Lauyan Atiku da
PDP, Levy Uzokwu, ya bukaci kotun zaben ya wajabtawa INEC ta basu daman bincike
cikin yanar gizo da na'urar 'Card Reader' da akayi amfani da su lokacin zabe.
Amma lauyan INEC, Yunus Usman, ya bukaci kotu tayi watsi da
wannan bukata inda yace: "Suna tambayarmu mu basu abinda bamu da
shi," Ya kara da jawo hankalin kotun da bukatar da PDP ta gabatar ranar 6
ga Maris cewa kayyayakin zabe kawai ta bukaci gani ba yanar gizo ba Jam'iyyar
PDP da Atiku Abubakar na kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari na APC a
zaben shugaban kasan da ya gudana ranar 23 ga Febrairu, 2019.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
SIYASA