Yanzu na zabi a kirani da 'Fes ledi' ba matar shugaban kasa ba - Aisha Buhari


Legit Hausa

Shekara hudu bayan da Muhammadu Buhari yace matarshi bazata rike ofishin Fes ledi ba, Aisha Buhari matar tasa, a ranar Alhamis ta bukaci da a kirata da Fes ledi. Tun bayan da aka rantsar da Shugaba Buhari karo na farko a matsayin shugaban kasar Najeria, ana kiran mai dakin nasa da matar shugaban kasa.

Amma matar tashi Aisha ta ce daga yanzu mukamin nata ya koma Fes ledi. Ta ce wannan zai magance rudanin da aka sanyawa matan gwamnoni game da mukamin da suke dashi a jihohinsu. Ta ce "A lokacin da aka zabi mijina karo na farko, ni na bukaci da a kirani da matar shugaban kasa."

"Amma na lura cewa hakan ya kawo rudani dangane da yadda za a rinka kiran matan gwamnoni a jihohinsu." "Sabida haka ina rokon ku gafara dangane da rudanin da na kawo, amma yanzu na zabi da a kirani da Fes Ledi." a cewarta.

Wannan matsayar ta matar shugaban kasa ya sabawa alkawarin da shugaba Buhari yayi a 2014 lokacin da yake takara, na cewa ba za ayi ofishin Fes Ledi a gwamnatinsa ba. a wata hira da buhari yayi da jaridar weekly Trust a cikin watan Satumba 2014, ya ce wannan ofishin na Fes Ledi babu shi a kundin tsarin mulki kuma ya kamata a bari ministirin mata tayi aikin ta ba tare da shiga huruminta ba. A lokacin ne Aisha Buhari ta bukaci da a kirata da matar shugaban kasa.

Koma de wane suna ake yin amfani da shi, karfin ofishin Aisha Buhari daya yake da na tsofaffin matan shugabannin kasa, a wani rahoto da ICIR ta fitar. Bugu da kari, yanzu har sunan ana tsammani zai canza.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN