Legit Hausa
A yayin sabunta ta'addanci, wani harin 'yan fashin daji da
ya auku a kwana kwanan nan ya salwantar da rayukan kimanin mutane 34 cikin
kauyukan Tungar Kafau da kuma Gidan Wawa dake karkashin karamar hukumar
Shinkafi a jihar Zamfara.
Sai dai wasu mazauan yankin Shinkafi sun ce mutane da aka
kashe sun kai 42, inda a ranar aukuwar harin aka samu gawawwakin mutane 40 kuma
daga bisani aka tsinto karin gawawwaki na mutane biyu.
Da take bayar da tabbacin aukuwar harin, hukumar 'yan sandan
jihar Zamfara ta ce 'yan ta'adda sun tarwatsa mutane ta hanyar harbi na
harsashin bindiga kan mai uwa da wabi cikin kauyukan biyu da misalin karfe 5.00
na Yammacin ranar Juma'ar da ta gabata. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar
Muhammad Shehu yayin gabatar da shaidar sa ga manema labarai, ya ce tuni
tarzoma ta lafa a kauyukan biyu na Tungar Kafau da kuma Gidan Wawa, inda
kwamishinan 'yan sanda na jihar, Usman Nogogo yayi tattaki wajen kai ziyarar
gani da idanu.
Jaridar BBC Hausa ta bayar da shaidar cewa, wannan ita ce
aukuwar hari na baya baya cikin hare-haren 'yan fashin daji da suka addabi
jihar Zamfara da kuma sauran jihohi musamman jihar Katsina dake makwabtaka da
ita. A yayin da a halin yanzu wasu mutanen Tungar Kafau da na Gidan Wawa suka
nemi mafaka a manyan garuruwa dake ciki da wajen jihar Zamfara, a baya aukuwar
wani mummunan hari a kauyen Kanoma da ya janyo salwantar rayuka ya yi sanadiyar
dakatar da wani Basarake da kuma hakimi a yanki.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi