Yakubu Danladi, wani matashi mai shekaru 34, ya zama kakakin majalisar dokoki


Legit Hausa

Yakubu Saliu Danladi, matashi mai shekaru 34, ya zamam shugaban majalisar dokokin jihar Kwara.Wannan shine karo na farko da Danladi ya fara zuwa majalisar dokokin bayan ya lashe zabe a karkashin inuwar jam'iyyar APC daga mazabar Ilesha-Gwanara. 

Honarabul Saheed Popoola, mamba a majlisar daga mazabar Balogun-Ojomu da ke karamar hukumar Offa, ne ya fara bayyana sunan Danladi a matsayin wanda zai jagoranci majalisar kafin daga bisani ya samu goyon bayan abokinsa honarabul Haliru Danbaba. 

Da ya ke karbar mukamin shugabancin majalisar, Danladi ya bayyana cewar ya sadaukar da kansa domin hidinmta wa majalisar da jihar Kwara. Da yake gabatar da shi a gaban ragowar mambobin majalisar, Popoola ya ce an haifi Danladi, mamba daga mazabar Ilesha/Gwanara a karamar hukumar Baruten, a ranar 31 ga watan Mayu na shekarar 1985 a garin Gwanara.

Ya yi karatun makarantar Firamare a Gwanara daga shekarar 1988 zuwa 1993, daga nan ya tafi makarantar Sakandire ta St Anthony dake garin Ilorin, wacce ya kamma a shekarar 2001. Ya yi karatun difloma da babbar difloma a bangaren injiniyarin a kwalejin kimiyya ta kasa da ke garin Kaduna (KADPOLY) daga shekarar 2003 zuwa 2008.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN