Legit Hausa
Hakaito jawabin ma'aikatan fadar White House, jaridar New
York Times, ta ruwaito cewa Trump ya bada umurnin kaiwa Iran hari wasu wurare
da dama wanda ya hada da na'urorin ganin jirage da yammacin ranar Alhamis, amma
ya canza ransa daga baya.
Har jiragen Amurka sun tashi sama domin zantar da hukuncin
shugaban kasan kafi ya canza ransa, New York ta samu rahoto daga wani jami'in
gwamnati. Jaridar Washington Post da tashar ABC sun bada rahoton cewa lallai
hakan ya faru saboda labarin ya fito daga bakin wasu ma'aikatan White House.
Mun kawo muku rahoton cewa Kasar Iran ta baro jirgin leken
asirin kasar Amurka yayinda rikici ke cigaba da kunno kai tsakanin manyan
kasashen guda biyu. Yayinda jami'an tsaron kasar Iran na ikirarin cewa jirgin
Amurkan ta shiga huruminta shi yasa suka barota, amma jami'an Amurka sun ce ba
haka bane, jirgi bata shiga hurumin Iran ba a lokacin.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
TSARO