Yadda Wata mata ta yi garkuwa da kanta domin ta tarawa mijinta kudi

Legit Hausa
Wata mata mai suna Misis Yemi Samuel a ranar Laraba, 26 ga watan Yuni ta bayyana cewa ta shirya garkuwa da kanta ne a kokarinta da tara kudi daga yan uwanta domin tallafa wa mijinta.
Matar wacce rundunar yan sandan jihar Kwara ta gurfanar tace mijinta ya kasance dan fansho a karkashin gwamnatin jihar Kogi sannan cewa shekaru da dama bai samu karban fansho dinsa ba, inda hakan yasa rayuwa tayi masu wahala.
Samuel ta ci gaba da bayanin cewa yan uwanta da ke da hali sun ki taimaka masu, don haka ta shirya garkuwa da kanta.
“Na yi hakan ne domin taimaka wa mijina wajen tara kudi da zai fara kasuwanci tunda gwamnatin jihar Kogi ta ki biyansu kuma yan uwanmu ma sun ki tallafa mana. Na san cewa yan uwanmu na da kudi kuma za su hada kudi idan na fada masu cewar anyi garkuwa dani,” inji ta.
Matar wacce ta tsere zuwa Ilorin don buya a gidan da suka yi haya ta bayyana cewa suna da zama a jihar Kogi don haka ta yanke shawarar zuwa ta boye a Ilorin tunda babu wanda ya san ta a chan.
“Na nemi a biya fansar naira miliyan daya amma sai aka kama ni. Na san cewa na aikata ba daidai ba amma ta haka ne kawai zan iya samun kudi tunda na kasa samun aiki bayan kammala karatun digiri,” cewar ta.
Kwamishinan yan sandan jihar yayinda yake gurfanar da ita tare da sauran masu laifi, CP Kayode Egbetokun yace Samuel ta yi garkuwa da kanta amma aka kama ta a Kulende, yankin Sango da ke Ilorin bayan ta nemi a biya N5,000,000.
Yace ba da jimawa ba za a gurfanar da ita a gaban kotu.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN