Yadda masarautu 584 ke hadidiye biliyoyin naira cikin kowace shekara a Arewacin Najeriya

Legit Hausa
Jihohi 19 da Arewacin Najeriya ya kunsa da kuma babban birnin kasar nan na Tarayya Abuja, su na batar da makudan kudi na biliyoyin nairori a kan masarautu da yankin ya kunsa cikin kowace shekara kamar yadda bincike ya tabbatar.
Binciken manema labarai na jaridar Daily Trust ya tabbatar da cewa, akwai kimanin masarautu 548 a fadin yankin Arewa da kuma garin Abuja inda ta fuskar girma 174 suka kasance manyan masarautu, 130 a mataki na biyu, 205 a matakin uku da kuma 37 a mataki na karshe.
Bayan wannan adadi na Sarakai, akwai kuma dubunnan dagatai, masu gari, da kuma masu unguwanni dake karkashin kulawa da kuma gudanarwar manyan masarautu a yankin Arewacin Najeriya.
Ba boyayyen abu bane cewa, Sarakunan gargajiya ba su da wani nauy na musamman da kundin tsarin mulkin kasar nan ya yi masu tanadi, illa iyaka kasancewar su ababe na riko da gargajiya da kuma raya al'adu a cikin al'ummomi daban daban.
Kazalika Sarakuna sun kasance jakadu na wanzar da zaman lafiya da kuma kawo sulhu a tsakanin al'ummomin su wajen gargadi da wa'azi gwagwardon iko duba da kasancewar su iyayen kasa.
A baya dai gabanin sauya tsarin mulki a kasar nan, Sarakunan gargajiya sun kasance masu kula da wasu hukumomi a kasar nan da suka hadar da 'yan sanda, gidajen yari, alkalanci da shari'a, ilimi da kuma dukkanin harkokin kudi da suka shafi masarautun su.
Babu shakka sarakunan gargagiya a Najeriya na da tasirin gaske a yayin da mafi akasarin su suka kasance tsaffin dakarun tsaro, gwamnoni, alkalai, ministoci, manyan ma'aikatan gwamnati da kuma tsaffin manyan ma'aikatan banki da kuma hamshakan 'yan kasuwa.
Sarakunan gargajiya su kan samu kudaden gudanar da harkokin masarautun su na yau da kullum daga gwamnatin jiha da kuma kananan hukumomi wajen biyan albashi, inganta fada, motoci da kuma sauran ababen bukata na fada.
A bisa al'ada, sarakunan gargajiya su na karkashin kulawa da kuma jagoranci na shugaban karamar hukumar da fadar su ta kasance. Kowace fada ta bambanta da takwarar ta wajen gudanar da al'amura ta fuskar batar da dukiya.
A yayin da girman masarautun yankin Arewa suka bambanta da juna, kowa ce fada ta bambanta da 'yar uwarta ta fuskar kashe kudi inda cikin bugun misali fadar Kano ke lashe fiye da Naira biliyan daya a kowane wata wajen biyan albashi kamar yadda tsohon kwamishinan kananan hukumomi na jihar Murtala Sule Garo ya bayar da tabbaci.
Kamar yadda tsohon kwamishinan kananan hukumomi na jihar Neja Halliru Zakari ya bayar da shaida, a watan Afrilun 2018, masarautar jihar Neja ta batar da kimanin naira miliyan 374 wajen sayawa masu daurin rawani motoci daban daban gwargwadon mukami da kuma mataki a fadar.
A can birnin Shehu kuma, gwamnatin jihar Sakkwato ta mallaki wani gidan saukar baki na naira miliyan 750 a shekarar 2016 cikn garin Abuja domin shakatawa da kuma saukar mai martaba sarkin musulmi a yayin da wani uzuri ya kai shi garin Abuja tare da tawagar sa.
Kafofin watsa labarai da dama a kasar nan sun ruwaito cewa, a yayin da fadar Zamfara ta kunshi masaurautu 17 a matakai daban daban, gwamnatin jihar a shekarar da ta gabata ta salwantar da dukiya ta kimanin naira miliyan dari biyar wajen gina sabuwar fada a masarautar Gusau ta Sarkin Katsinan Gusau.
A jihar Katsina kuma, bincike ya tabbatar da cewa manyan masarautu biyu na Katsina da na Daura na samun abin dogaro na kimanin kaso biyar cikin dari na adadin dukiya da kananan hukumomi 29 na jihar ke samu a kowane wata.
Kamar yadda sakataren gwamnatin jihar Jigawa Abdulkadir Fintiri ya bayyana, hakan take ga masarautu biyar da jihar ta kunsa da suka hadar da Dutse, Hadejia, Kazaure, Gumel da kuma Ringim.
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN