Legit Hausa
Kwamitin bin diddigi wanda jam’iyyar All Progressives
Congress (APC) ta nada domin gano matsalolin da jam’iyyar ta fada har yayi
sanadiyar mummunar kaye da ta sha a zaben 2019 ta gabatar rahoton ta.
A cewar kwamitin tsarin yadda tsohon gwamnan jihar Zamfara,
AbdulAziz Yari ya ja ragamar jam’iyyar na daya daga cikin babban dalilin da ya
sa aka yi ta samun matsaloli a jam’iyyar da ya kai ga har ta sha kaye a
zabukkan a aka yi a baya. Har ila yau, kwamitin ta ce ta samu labarin zagon
kasa da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa reshen Arewa, Sanata Lawal
Shuaibu ya rika yi wa jam’iyyar.
Sakataren APC reshen jihar Zamfara, Mohammed Bakyasuwa ne ya
bayyana hakan yayinda yake zantawa da manema labarai a Abuja. "Ina so kowa
ya kwana da sanin cewa tsakaninmu da bangaren Yari ba’a ga maciji yanzu saboda
kuwa anja daaga. Yari ne shafaffen da ya saka jam’iyyarmu cikin kalubalen da
muka tsinci kanmu a yanzu.
“Yanzu dai mun dauki matsaya guda cewa daga yau, mun kori
AbdulAziz Yari da Sanata Lawali shu’aibu daga APC,. Kowa ya sani kuma wannan
shine matsayar mu ‘yan jam’iyyar APC na Zamfara
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
SIYASA