Wasu 'yan bindiga sun tarwatsa masu 'sallar Tahajjud' a Maiduguri

BBCHausa

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hari ana tsakar Sallar dare a birnin Maiduguri jihar Borno.

An kai harin ne a babban masallacin Juma'a da ke unguwar Sajeri can bayan garin Maiduguri.
Wasu mazauna unguwar wadanda suka tabbatarwa da BBC da faruwar lamarin sun ce 'yan bindigar sun shigo ne misalin karfe daya na dare bayan an fara sallar Tuhajjud.

Daya daga cikin mazauna unguwar wanda ya ce yana makwabta da masallacin ya ce, yana cikin alwala a gida yana shirin shiga masallaci ya ji an fara harbin bindiga.

Ya ce yana kyautata zaton 'yan Boko Haram ne, inda ya ce "suna ta kabbara, sun kewaye masallaci suna ta cewa Allahu Akbar, Allahu Akbar."

"Bayan sun kewaye masallaci suka fara harbi ta sama, sai mutane da ke cikin masallacin suka fara gudu," in ji shi

Sai dai ya ce ba su kashe kowa ba, amma albarushi ya samu wasu daga cikin wadanda ke gudu.
Sannan sun saci wayoyin mutane da dama wadanda tsoro ya sa suka bari a cikin masallaci.
Ya ce wayar matarsa na cikin wadanda 'yan bindigar suka dauka.

Mazauna Sajeri sun ce ko da aka kawo harin babu jami'an tsaro a unguwar, sai daga baya 'yan kato da gora suka zo da kuma sojoji da suka zo da asuba.

Sun ce da safe sabon gwamnan jihar ya shigo unguwar inda ya yi masu jaje.
Wasu na tunanin 'yan fashi ne suka shiga unguwar ba 'yan Boko Haram ba, inda suka ce sun saci shanu baya ga satar wayoyin mutane a masallaci.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN