Legit Hausa
An kama wani yaran gida mai suna Joseph Ogbu dan shekara 22
bayan da ya caka ma uwar dakinsa, Oreoluwa John, mai dauke da juna biyu wuka
wanda haka yayi sanadiyyar mutuwarta, sa’annan kuma ya shake mahaifiyarta mai
shekaru 89, Adejoke John, a gidansu Mai lamba 4 layin Ogunlana, Surulere,
Lagos.
Bayan nan, sai Ogbu, wanda dan asalin karamar hukumar Oju ne
dake jihar Binuwe, ya dauke wayoyin iyayen gidan nasa da wasu abubuwa masu
tsada, sa’annan yayi kokarin guduwa cikin motar uwar dakin tasa. Mazauna
unguwar sun bayyana cewa a lokacin da ya ke kokarin tserewa, yayi kokarin ya
banka ma gidan wuta ta yadda al’amarin zai nuna kamar gobara ce akayi.
A lokacin da Vanguard ta ziyarci wajen, wata Rasheedat
Ganiyu ta ce “A lokacin da yake fitowa daga gate din gidan, yan kungiyar Odua
sun tuhume shi da ya gaya masu ina zashi yake sauri haka. “Sai yake fada masu
da turancin Pidgin cewa ‘Uwar gida ce ta aike ni’. Amma yan kungiyar na tunanin
akwai wani abu dai saboda yadda muryarshi ke kyarma, sai suka tilasta mashi da
a koma saman bene. A lokacin da suka bishi saman benen, sai suka tarar da uwar
da diyarta zube a kasa.”
A lokacin da yake bayyana yadda akai ya kashe uwar dakin
tasa, Ogbu ya ce “An dauke ni aiki ranar Talata. Ranar laraba da misalin karfe
9:00 na dare, uwar gida ta kirani tace in tsaftace gidan. “Sai na gaya mata
cewa zanyi washe gari saboda yanzu dare yayi.
Amma sai ta nace sai na gyara gidan. Hakan ya jawo cece-kuce
wanda a lokacin na fusata. Na caka mata wuka amma ban taba mahaifiyarta ba. Da
kanta ta mutu.” An tambayeshi ko ina zai kai motar Oreoluwa da kayan da ya
dauka, sai ya ce “Na rude a wannan lokacin, ban ma san inda zani ba.’" Mai
magana da yawun hukumar yan sanda ta jihar Legas, DSP Elkana Bala, ya tabbatar
da afkuwar lamarin.
Ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa daga ofishinsu na
Surulere da misalin karfe 3:00 na dare akan afkuwar lamarin. Ya ce “Duba da
cewa duk sun mutu, yayi kokarin guduwa inda ba za a gano shi ba. Amma yan sanda
dake zagaye a Ogunlana suka damke shi
.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi