Legit Hausa
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Ba wannan ne karo na farko da aka taba yashe wata rijaya
wadda tayi sanadiyyar mutuwar mutane hudu ba a Sokoto. Wannan ne karo na uku
tun bayan da aka haka rijiyar kimanin shekara daya da wata biyu, amma wannan
karon abun ya zo da hadari wanda ya bar al’ummar kauyen Baichi da ke garin Yabo
a karamar hukumar Yabo ta jihar Sokoto cikin jimami.
Jaridar Daily Trust, ta gano cewa biyu daga cikin mamatan,
uba da da, kwarrarun maginan rijiya ne. Lamarin ya faru ne da misalin karfe
9:00 na safe a lokacin da wani mazaunin kauyen da aka bayyana a matsayin malam
Aliyu Shekare ya kira wani maginin rijiya da aka fi sani da Mai Zuma, don ya
yashe masa rijiyarsa.
Mai Zuma, wanda maginin rijiya ne kuma mai saida zuma, ya
taho tare da dansa, ya shiga rijiyar tare da injin na jan ruwa don ya fitar da
laka daga cikin rijiyar wanda sanadiyyar hakan ya rasa iskan shaka ya mutu.
Daily Trust ta binciko cewa shima dan nasa ya mutu a cikin
rijiyar a lokacin da yake kokarin ceto rayuwar mahaifin nasa. Wani mazaunin
kauyen ya bayyana cewa “Mahaifin ya nemi taimako a lokacin da ya rasa iska ya
jikata zai mutu, wanda hakan yasa dan nasa ya fada rijiyar don ya ceto
mahaifin, amma shima sai ya rasa iska ya shake ya mutu.
Malam Aliyu Shekare ya bayyana cewa “Na tsorata na gigice
bayan da nasamu wannan mummunan labari. Mai zuma ne ya gina mani wannan
rijiyar. Kuma ba wannan ne karo na farko da na taba kiranshi ya yashe mani
rijiar ba. Wannan ne karo na uku. Rijiyar na da tsawo taki takwas da rabi kuma
duk sauran lokuttan Mai zuma ya yashe mani ita lafiya lau.”
Sauran mutum biyun da suka rayukansu sune Yahya Shanu wani
malamin makaranta, yana da mata da yara biyu, dayan kuma shine Zaharadden Dodo,
wanda ya kammala karatunsa a jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto, kuma ya
shirya tsaf zai tafi bautar kasa a jihar Osun washe garin ranar.
Yan kauyen sun kira masu kashe gobara wanda suka zo kuma
tare da taimakon yan su, aka samu aka fitar da gawawwakin da misalin karfe 2:00
na rana. Wani daga cikin jami’an kashe gobara na sokoto ya tabbatar da cewa mamatan
sun rasa iska ne sakamakon hayakin injin din jan ruwa da ake amfani dashi cikin
rijiyar.
Mai garin kauyen na Baiche, Malam Muhammadu Dan Magaji ya ce
wannan ne karo na farko da irin wannan ifila’i ya afku tun da ya hau mulki
kimanin shekaru 16 da suka wuce. Mai garin ya kara da cewa sun mika lamarin ga
ubangiji kuma zasu cigaba da mafani da rijiyar da aka rufe tun bayan afkuwar
lamarin. Ya ce” Da rijiyar da ruwan ciki duk basu da illa.”
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
BIRNIN-KEBBI