Wani matashi dan shekara 29 ya halaka kansa a jihar Kebbi


Legit Hausa

Wani matashin dalibi dan shekara 29 na Waziri Umaru Federal Polytecnic , Birnin kebbi kuma mazauni a unguwar badariya, wanda aka bayyana a matsayin Solomon Benedict ya halaka kansa a dalilin matsanancin talauci. Benedict dai ya halaka kansa ne ta hanyar shan maganin kwari a cikin madarar yogut. 

Abokananshi sunyi kokarin ceto rayuwarshi amma abin yaci tura. A lokacin da yake zantawa da yan jarida ranar Talata, 11 Yuni 2019, wani aboki marigayin ya bayyana cewa “ mun lura da cewa bashi da sauran sukuni. Ya kama cikinsa sai daga baya muka lura cewa ya gauraya maganin kwari cikin abin shansa. Ya rasa ransa kafin mu ceto shi." 

Bayanai sun nuna cewa matashin ya rasa ransa a lokacin da ake kokarin kaishi asibiti mafi kusa don ceto rayuwarshi. Wata abokiyar mamacin dake a garin Jega, ta zanta da yan jarida inda kuma ta bukaci a sakaye sunanta ta ce” tun da dadewa yake ce mani zai kashe kansa, idan matsanancin talaucin da yake fama dashi bai rage ba. Amma ban taba yadda da gaske yake ba. 

Na tuna duk sanda ya ziyarce ni a Jega, yana zanta mani akan matsin da yake fama dashi na rashin kudi, sai in bashi yan kudin mota da zai koma Birnin kebbi, kuma yakan gaya mani cewa idan lamarinshi bai inganta ba zai kashe kanshi." 

Ta kara da cewa "Nayi mamaki matuka lokacin da na samu kiran waya daga Sokoto ana fada mani cewa Solomon ya kashe kansa” Mai magana da yawun Hukumar yan sanda ta jihar Kebbi DSP Nafi’u Abubakar, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga yan jarida a lokacin da yake zantawa dasu ta waya a ranar Talata, 11 Yuni 2019. Yace ”kwarai muna da masaniya akan afkuwar lamarin. Yaron shekararshi 29. Ya halaka kansa a unguwar badariya dake Birnin Kebbi"
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN