• Labaran yau

  Wa'iyazubillah: An kama malamin jami'a tsirara yana kokarin yin zina da dalibarshi


  Legit Hausa

  A jiya Juma'a ne aka kama wani malamin jami'a dake koyarwa a bangaren aikin banki a jami'ar jihar Ekiti, dake Ado Ekiti, Dr. O.O Aduwo, tsirara haihuwar uwarshi yana kokarin yin zina da wata dalibarshi wacce aka bayyana sunanta da Nike, wacce ya gayyaceta zuwa gidansa a jiyan.

  A cewar wani rahoto da daliban jami'ar suka fitar, Dr Aduwo yayi kaurin suna wajen tilasta dalibansa mata domin suyi zina dashi. Jiya Nike da ita da saurayinta da kuma wasu abokananta suka hada baki akan taje gayyatar da malamin yake yi mata, kamar yadda ya nema, A lokacin da take cikin gida, saurayin Nike da kawayenta wadanda suka boye a kofar gidan malamin, sai suka shiga cikin gidan suka kama shi tsirara haihuwar uwarsa yana neman kwanciya da ita.

  A wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumunta, malamin ya tsorata sosai bayan an kama shi, an jiyo shi a cikin bidiyon yana rokar daliban da suka kama shi da su rufa masa asiri. A cewar daliban makarantar, Nike ce ta sanya bidiyon a shafinta na WhatsApp. Kwanakin baya ma an taba kama wani malamin jami'a wanda ya nemi dalibarsa da ta kwanta dashi kafin ta samu ta ya tsallakar da ita jarrabawa. Allah ya kyauta.
   

  DAGA ISYAKU.COM

  Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

   Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wa'iyazubillah: An kama malamin jami'a tsirara yana kokarin yin zina da dalibarshi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });