Legit Hausa
Majalisar dattawa a jiya Alhamis, 13 ga watan Yuni tace a shirye take ta karbi duk wani umurni daga shugaban kasa Muhammadu Buhari. Majalisar dattawan ta tara wacce tayi zama na biyu a yanzu tace za ta tura wani sako zuwa ga Shugaban kasar ta ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya.
Majalisar dattawan ta kuma ce za ta aika wani sako zuwa ga
Shugaban kasar domin sanar masa cewa majalisar dattawa ta tara ta taru sannan
cewa an zabi shugabannin ta, Ahmad Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa,
da kuma Ovie Omo-Agege a matsayin mataikain Shugaban majalisar dattawan.
Sanatocin sun kuma yanke shawarar aika wasikar taya murna ga
kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da mataimakin kakakin majalisar
wakilai Ahmed Idris Wase a bisa nasara da suka yi da kuma sanar masu da zaben
Lawan da Omo-Agege.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi