Umar Namashaya Diggi ya karfafi tsaro na Vigilante da mota, babura 10 a karamar hukumar Kalgo

Shugaban karamar hukumar mulki ta Kalgo a johar Kebbi Alh. Umar Namashaya Diggi, ya bayar da tallafin motar sintiri tare da sababbin babura guda goma ga rundunar sa kai na banga Vigilante da ke karamar hukumar Kalgo ranar Laraba.

Alh. Umar Namashaya Diggi, ya kasance a jerin sahun farko da ya fara aiwatar da umarnin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu, wanda ya bukaci shugabannin kananan hukumomi a jihar Kebbi su tallafa ma Vigilante domin inganta tsaro a fadin jihar.

An gudanar da taron mika makullan motar da babura a harabar Sakatariyar karamar hukumar Kalgo, wanda ya sami halarcin Ubannin kasar Kalgo, Nayelwa,da Kuka, wanda su ma sun mika makullai ga wadanda suka amfana da tallafin.

Daga cikin yan Vigilante da suka amfana da shirin na yau, sun hada da:

1. Ibrahim Muhammed -- Kalgo .
2. Umaru Ubandara Hirishi -- Badariya/Magarza
3. Shayau Dangoma -- Dangoma Gayi
4. Sahabi Mota Diggi -- Diggi
5. Muhammadu Gayya  --Zuguru
6 Bello Sarkin Yaki  --Wurigauri
7. Muhammad Yafi  -- Mutubari
8. Maidaji Sahabi  -- Etene
9. Musa Uban Daba  -- Kuka
10. Bala Garba  -- Nayelwa

Taron ya sami halarcin manya da suka hada Kwamandan rundunar tsaro ta NSCDC H. Ringim, Uban kasar Kalgo Alh. Haruna Jada Rasheed tare da Ubannnin kasar Nayelwa, kuka da sauran Ubannin kasa, sai Hon. Ahmed Bawa, da kuma DPO na yansandan karamar hukumar Kalgo Yakubu Rumu, sai mataimakin kwamandan rundunar Vigilante na jihar Kebbi  Abubakar Sambawa

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN