Legit Hausa
Akwai kwararan alamu da ke nuna tsohon gwamnan Legas,
Akinwunmi Ambode, da takwarorinsa na Adamawa da Bauchi, Mohammed Bindow da
Mohammed Abubakar suna cikin wadanda za a nada ministoci a sabuwar gwamnatin
Buhari.
Saturday Punch ta ruwaito cewa shugabanin jam'iyyar All
Progressives Congress (APC) sun yanke shawarar cewa dukkan gwamnonin jam'iyyar
da ba su zarce kan mulki ba za su samu kujerar minista a sabuwar tafiyar da za
ayi. Ambode da Bindow da Abubakar ba su yi nasarar zarcewa kan karagar mulki a
jihohin su ba.
Ahmed Lawan, sakataren shirye-shirye na jam'iyyar APC ya
tabbatar da wannan batun. Lawan ya ce kawo yanzu shugabanin jam'iyyar ba su
nemi jihohi su tura sunan ministoci ba amma ya ce akwai yiwuwar za a nada
Bindow minista saboda umurnin da shugabanin jam'iyyar na kasa suka bayar.
Bindow ya sha kaye ne a hannun Ahmadu Fintiri na jam'iyyar Peoples Democratic
Party (PDP) bayan an yi zaben kece raini.
Lawan wanda ke neman kujerar sakataren jam'iyyar na kasa ya
ce, "Wannan shine matsayar da shugabanin jam'iyyar suka cimma, babu wanda
za a zaba bayan Bindow. Ba su nemi mu aika suna ba. Wannan shine tsarin; duk
wata jiha da gwamna bai ci zabe ba, za a nada gwamnan minista."
Idan aka yi la'akari da wannan matakin, Ambode da ya rasa
kujerarsa ga Mista Babajide Sanwo-Olu da Abubakar da ya rasa kujerarsa ga Bala
Mohammed suna iya zama ministocin da za a zaba daga jihohin su. Majiya daga
fadar shugaban kasa ta ce Buhari da na kusa da shi suna goyon bayan Ambode
saboda haka ana kyautata zaton zai kasance cikin sabbin ministocin.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi