Tirkashi: Shugaban hukumar 'yan sanda ya tura karnuka suyi gadin tashar jirgin kasa

Legit Hausa

Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya bada tabbaci bajama’ar da ke amfani da jiragen kasa cikakken tsaro a dukkan lokaci tare da tura karnukan yan sanda zuwa tashoshin jirgin kasa a fadin kasar.
A wani taro da aka gudanar a Abuja a ranar Talata, 25 ga watan Yuni, shugaban yan sandan yace jami’an K-9 squad sun samu cikakkiyar horaswa musamman don bincikar ayyukan masu safarar kwayoyi da sauran laifuffuka wadanda ke son suyi anfani da jirgin sama a matsayin hanya mafi sauki wajen cimma burinsu.
Ya bayyana cewa hakan na daga cikin shirin ‘Operation Puff Adder’ kuma ana sanya ran zai dace da ayyukan matakan tsaro a fadin kasar.
Ya bayyana a jawabinsa cewa “Ina son inyi amfani da wannan damar in yaba ma jami’an rundunan yan sandan Najeriya akan hadayan su a aikin Operation Adder, biyayya, Jajircewa ga aiki da kuma kwarewa wanda a halin yanzu ya taimaka a tafiyar ayyukan wajen cimma burinta na tabbatar da daidaituwar lamarin tsaro.
“Ina matukar farin ciki akan nasarorinku, duk da haka ina bukatar ku da ku cigaba a tafarkin nasara, inda ya bayyana cewa laifi abu ne da ake aikatawa kullun kuma ko da yake mun samu nasarori kwarai da gaske, baza mu so rage yawan matakan tsaronmu ba.
“Ina rokon Allah madaukakin sarki ya cigaba da kare ku gaba daya a duk lokutan da kuke sadaukar da kanku a aikin samar ma al’umman kasarmu tsaro.”
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN