Tirkashi: Dumu-dumu na iske mahaifiyata na zina da limamin mu a cikin gidanmu - Wata budurwa ta koka


Legit Hausa

Wata kwararriya a fannin zamantakewar ma'aurata, Joro Olumofin, ta bada labarin wata matashiyar budurwa, wacce ta bayyana cewa ta shiga gidansu ta iske limamin cocinsu tare da mahaifiyarta suna zina a cikin gidansu.

A cewar budurwar, ta ce ta dawo gida da rana, kawai sai ta iske mahaifiyarta da limamin cocinsu suna holewa a cikin gidansu. Budurwar ta kara da cewa kawai ta fita ta bar gidan ne saboda bata san me zata ce ba a wannan lokacin. Budurwar a karshe ta yi tambaya akan, shin yana da kyau mahaifiyarta ta kawo kato har cikin gidansu ko kuwa babu? Ga abinda budurwar ta sanya a shafinta na sada zumunta:

"Dan Allah ina neman taimakon shawarwarin ku. Na dawo gida da rana, kawai sai na iske mahaifiyata da limanin cocin mu suna zina aa tsakar gidanmu, dole ya sanya ni ficewa daga gidan saboda ban san me zance ba a wannan lokacin.

"Shin yana da kyau ma ta dinga kawo kato har cikin gidanmu, kuma shima limamin namu munafiki ne, shine mutumin da yake yi mana wa'azi cewa zina babu kyau a koda yaushe. Gaskiya kai na ya daure na rasa yadda zanyi," in ji budurwar.
 

DAGA ISYAKU.COM

 Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN