Legit Hausa
Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye,
ya kara zuwa da wani sabon al'amari akan sabon zababben mataimakin majalisar
dattawa na kasa, Sanata Ovie Omo-Agege akan abinda ya faru na daukar sandar
girma a majalisa shekarar da ta gabata.
Sanatan ya sanya hoto a shafinsa na Instagram, shi da sabon
shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan da Omo-Agege, da kuma wani ya
rike sandar da hannu biyu, Melaye ya kara da cewa Lawan yana sanarda da mai
rike sandar cewa: "Ka rike sandar nan da hannu biyu, saboda ban yadda da
wannan Omo-Agegen ba, barawo ne."
A hoton ya nuna yadda wanda ke rike da sandar ya maidawa
shugaban majalisar martani da cewa: "Yallabai kada ka damu na rike shi da
kyau da kyau." Haka kuma Melaye ya kara rubuta wani abu a kasa inda yake
cewa: "Idan kana aiki da barawon sanda." Shekarar da ta gabata ne
wasu 'yan daba suka kutsa kai cikin dakin majalisar dattawa suka dauke sandar
da ake zartar da hukunci da ita.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI