takaitaccen tarihin marigayi Janar Sani Abacha yayinda ya cika shekaru 21 rasuwa a yau


Legit Hausa

A yau Asabar, 8 ga watan Yuni ne, tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Sani Abacha ya cika shekaru 21 da mutuwa. An haifi Janar Sani Abacha ranar 20 ga watan Satumbar shekarar 1943 a cikin garin Kano. 

Ya yi makarantar Firamari a makarantar City Senior Primary School, Kano, sannan ya garzaya Government College, Kano, 1957-1962, daga nan kuma ya tafi makarantar Kwalejin horas da sojoji ta Kaduna Najeriya, 1962-1963. Sannan ya wuce kwalejin Horas da Sojoji ta Aldershot dake Ingila, 1963, Kwalejin horas da dakarun kasa ta Warminster, ta Birtaniya 1966, 1971 Kwalejin sojoji ta Jaji dake Kaduna Nijeriya, 1976, Kwalejin nazarin manufofi da tsara dabarun mulki ta Kuru, Jos, 1981, ya yi kuma wasu kwasa-kwasai da suka shafi harkar tsaro a Canada, Amurka a shekarar 1982 

Tun daga juyin mulki na farko a Najeriya a shekarar 1966 janar Sani Abacha ke taka rawar gani sai wanda aka yi wa Shagari da na Babangida da kuma wanda yaiwa Cif Ernest Shenakon. Allah ya yiwa Janar Sani Abacha rasuwa ranar 8 ga watan Yuni shekarar 1998 yana da shekaru 54 da haihuwa sakamakon ciwon zuciya. Ya rasu ya bar mata daya Hajiya Maryam Abacha da 'ya 'ya tara mata uku da maza shida.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN