Sunaye: Rundunar sojin Najeriya ta kashe mutane 9 da ke yada labaran boko haram


Legit Hausa

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe mutane 9 dake watsa labaran kungiyar Boko Haram, wacce da ta rikide zuwa ISWAP, a kafafen sadarwa da dandalin sada zumunta. Sagir Musa, darektan yada labarai da hulda da jama'a na rundunar sojin Najeriya, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar. 

Ya ce kashe 'yan kungiyar sadarwa na kungiyar Boko Haram ya tabbatar da cewar rundunar soji ta gama gurgunta dukkan aiyukan kungiyar. Ya lisafa sunayen mutane 9 da aka kashe kamar haka: Abu Hurayra al-Barnawi, Ali alGhalam al-Kajiri, Abu Musab Muhammed Mustafa al-Maiduguri, Abu Abdullah Ali al-Barnawi, da Abu Musa al-Camerooni. Ragowar sune; Ahmed al-Muhajir, Abu Ali al-Bamawi, Abu Khubayb bin Ahmed al-Barnawi da Abu al-Qa'qa' al-Maiduguri.

 "Kowa ya san kungiyar na amfani da kafafen yada labarai domin yada farfaganda a kokarinta na kafa daular mulki irin nata," a cewar sa. Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar tun a shekarar 2009 kungiyar Boko Haram ta fara amfani da kafafen sadarwa, musamman a dandalin sada zumunta, domin yada faifan bidiyo da lakcoci domin jan hankalin matasa daga kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi su shiga kungiyar. 

NAN ta kara da cewa kungiyar ta canja salo a shekarar 2014 ta hanyar bude shafuka da dama a dandalin sada zumunta irin su 'Facebook' da Tuwita domin isar da sakonni da kuma tuntubar jama'a.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN