Sojoji Sun kama rikakkun masu garkuwa da mutane guda 5 a Katsina (Hotuna)


Legit Hausa
Dakarun sojin Najeriya na rundunar atisayen HARBIN KUNAMA III sun yi nasarar kama wasu 'yan bindiga dake satar mutane domin garkuwa da su da kuma aikata fashi da makami. Rundunar sojin ta kama mutanen ne yayin wani atisaye da ta gudanar a kauyen Sheme da hanyar zuwa dajin Ruwan Godiya da makwabatan kauyaka dake karkashin karamar hukumar Faskari. 

A sanarwar da kanal Sagir Musa, mukaddashin darektan yada labaran rundunar soji, ya fitar a shafin rundunar soji dake 'facebook', ya ce dakarun soji sun gudanar da atisaye a kauyen ne bayan samun sahihan bayanan sirri a kan aiyukan 'yan ta'addar da suka addabi kananan hukumomin Funtua da Faskari. 

Rundunar soji ta kafa runduna ta musamman tare da tura ta karamar hukumar Faskari domin kawo karshen aiyukan 'yan ta'adda da suka addabi kauyukan karamar hukumar ta Faskari da karamar hukumar Funtua mai makwabataka da ita. Sagir Musa ya bayyana cewar dakarun sojin sun yi nasarar kama wasu 'yan ta'adda guda biyar a kauyen Sheme dake kan hanyar zuwa dajin Ruwan-Godiya tare da bayyana cewar yanzu haka dakarun soji na cigaba da gudanar da atisaye a maboyar 'yan ta'adda dake yankin. 

Ya kara da cewa 'yan ta'addar da aka kama sun bayyana cewar sune ke aikata laifukan fashi da makami tare da satar mutane domin neman kudin fansa. Sun bayyana cewar suna aika mutanen da suka sace zuwa wurin shugabanninsu dake sansaninsu a cikin surkukin dajin Ruwan-Godiya.

"Sakamakon hakan, dakarun soji sun kara kutsa wa cikin dajin Ruwan-Godiya tare da kone sansanin 'yan bindiga yayin da mu ke cigaba da gudanar da atisaye domin farautar ragowar 'yan bindigar," a cewar sa. Kazalika, ya bukaci jama'a da suke bayar da sahihan bayanai ga rundunar soji a kan duk wani motsin 'yan bindiga da 'yan ta'adda domin daukan matakan gaggawa a kansu.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN