Sojoji 14 sun gurfana da laifin kisa da garkuwa da mutane a FatakwalLegit Hausa

Kamar yadda hukumar dakarun sojin kasa ta Najeriya ta bayyana a ranar Asabar 15, ga watan Yunin 2019, an fara gudanar da shari'ar wasu dakaru 14 a gaban kotun hukumar sojin mai tabbatar da da'a da kuma hukunci a kan dakaru.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, an fara gudanar da wannan shari'a a kan dakarun soji 14 bayan sun shiga hannu da zargin aikata miyagun laifuka na kisa, garkuwa da mutane da kuma wasu laifuka da suka sabawa kundin tsarin mulkin kasa. Yayin fara zaman kotun a karo na farko da aka kaddamar a birnin Fatakwal, babban jami'in soji mai kula da yankin na jihar Ribas, Manjo Janar Jamil Sarham, ya ce ababen zargin sun kasance kanana da kuma wasu manyan dakarun hukumar sojin kasa.

Manjo Janar Sarham ya ce kotun ta fara zamanta bisa ga tanadin sashe na 131 cikin kundin tsarin hukumar dakarun sojin kasar nan domin tabbatar da da'a da kuma kiyaye hukunce hukunce a tsakanin dakaru.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, laifukan wannan dakaru 14 sun hadar da kisa, garkuwa da mutane, kauracewa aiki, da kuma sabawa dokokin hukumar dakarun soji ta kasar nan da babu shakka an yi tanadin hukuncin cikin kundin tsari na hukumar da aka kaddamar tun a 2004. Babban jami'in na soji ya kuma kara da cewa, wannan hukuncin da kotun tabbatar da da'ar dakaru za ta zartar zai zamto izina da kuma jan kunne ga sauran dakaru masu mummunar manufa ta sabawa doka.


DAGA ISYAKU.COM

 Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN