Legit Hausa
Akalla zababbun sanatoci 61 ne suka shirya zabar Ahmed Lawan
a matsayin shugaban majalisar dattawa, cewar kungiyar kamfen dinsa a ranar
Asabar, 8 ga watan Yuni. Sakataren kungiyar, Barau Jibrin, ya karanto jerin
sunayen ga yan jaridar a Transcorp Hilton Abuja.
Mista Jibrin yace jerin sunayen ya hada 60 daga cikin
zababben sanatocin APC 62 da kuma daya daga jam’iyyar Young Peoples Party
(YPP). Yace a baya sunayen ya kai 64 amma daga bisani ya koma 62 sakamakon
hukuncin kotu a kan jihar Zamfara.
Ya nuna karfin gwiwar cewa sanatoci 61 za su zabi Mista
Lawan. Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa sanatoci 32 me kacal suka halarci
taron. A baya shugaban kwamitin kamfen din, Yahaya Abdullahi, ya yi watsi da
BATUN cewar Lawan na da izza kamar yadda wasu ke tunani.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi