Legit
Hausa
Shugaban
Najeriya Muhammadu Buhari ya nada wasu sababbin Alkalai a kotun kolin kasar.
Mun samu wannan labari ne a Ranar Lahadi 9 ga Watan Yuni, 2019, daga bakin
Malam Garba Shehu. Garba Shehu wanda ya kasance mai magana da yawun bakin
shugaban kasar, shi ya tabbatar da cewa shugaba Buhari ya nada wasu sababbin
Alkalai a babban kotun Najeriya da ke Garin Abuja.
Shugaban
kasar ya aikawa Alkalin Alkalan Najeriya na rikon kwarya takarda, inda yake
sanar da shi game da wannan mataki da ya dauka. Hakan na nufin Alkalan kotun
kolin sun kara yawa yanzu. Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa Muhammadu
Buhari ya dauki wannan mataki na kara yawan Alkalan da ke kotun koli ne kamar
yadda sashe na 230 na tsarin mulki ya ba sa cikakken iko.
Malam
Shehu wanda tun 2015 yake magana a madadin shugaban kasar ya ke cewa yanzu
akwai Alkalai 21 a teburin babban kotun kasar, wanda wannan shi ne asalin abin
da dokar Najeriya tayi tanadi. Mai magana da yawun bakin shugaba Buhari ya kara
da cewa wannan mataki da gwamnatin Najeriya ta dauka yana cikin kokarin da ta
ke yi na ganin shari’a na tafiya ba tare da kakkautawa ba.
Sai dai fadar
shugaban kasar ba ta bayyana sunayen wadannan Alkalai da ta nada zuwa kotun
kolin ba. A daidai wannan lokaci kuma shugaban kasar ya amince da murabus din
tsohon CJN, Walter Onnoghen.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI