Shuaibu ne ke yi wa Jam'iyyar PDP leken asiri - Shugabannin APC

Legit Hausa

Kwamitin Gudanarwa (NWC) na jam'iyyar All Progressives Party (APC) na kasa ta ce Lawan Shuaibu, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa, yankin arewa dan leken asiri ne na jam'iyyar PDP. Ahmad Suleiman Wambi, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa, yankin Arewa Ta Tsakiya, ya ce jam'iyyar za ta dauki mataki a kan Shuaibu kamar yadda This Day ta ruwaito.

Legit.ng ta gano cewa Wambi ya ce: "Ina fada muku, Shuaibu ne sanadin yawancin matsalolin mu. 'Yan waje na ganin laifin Oshiomhole amma ba su san cewa Shu'aibu ne babban matsalar mu ba. Kafin mu kammala taro, PDP sun san abinda muke tattaunawa.

"Kafin mu kammala taron mu, kowa ya san matakin da za mu dauka. Ya za ayi ka gina jam'iyya tare da dan leken asiri kamar Shu'aibu a jam'iyyar ka? Amma Allah ya tona masa asiri kuma za a tona dukkan laifukansa a rahoton da za a gabatarwa kwamitin ladabtarwa."

Da ya ke tsokaci kan zargin Oyegun, jigon na APC ya ce: "Zargin da Oyegun ya yi kan Oshiomhole ra'ayoyinsa ne. Oyegun yana fushi ne saboda an sauya shi da Oshiomhole. Oshiomhole ya fi shi shiri. Yana bakin ciki ne kawai saboda an zabi Oshiomhole a maimakonsa. Ba zai taba zama kamar Oshiomhole ba."

Da ya ke mayar da martani kan zargin da ake masa na zama dan leken asirin PDP, Shuaibu ya ce: "Wa na sani a PDP da zan rika bashi bayannan sirri? Mene na yi wa PDP? Na yi wa shugaba Muhammadu Buhari kamfe a jihohin daban-daban.

Saboda haka, mene ya sa za a ce ina yi wa PDP aiki? "Bayan ganin labarin, zan tafi kotu saboda su sanar da ni aikin da na yi wa PDP. Zai zo kotu ya fada min ayyukan da na yi wa PDP. Dama shi na hannun daman Oshiomhole ne."
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN