Sheikh Gumi ya bawa Kwankwaso kyautar iya jagoranci


Legit Hausa

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakala, da ragowar wasu mutane uku sun samu kyautar karrama wa ta musamman da gidauniyar Sheikh Gumi ke bayar wa ga shugabannin da suka nuna halaye nagari duk shekara. 

Ragowar mutane uku da aka karrama tare da Kwankwao da Wakala sune; Farfesa Abdulmumin Hassan Rafindadi, Kanal Yawale Iliyasu (mai ritaya) da Dakta Muhammed Suleiman Adam, babban limami a masallacin Sultan Bello kuma lakcara a jami'ar jihar Kaduna. 

Da yake mika kyautar gare su yayin rufe Tafsirin azumin wanna shekarar, Dakta Ahmad Gumi, dan marigayi Abubakar Gumi, ya ce ana bayar da kyautar ne ga jagororin da suka nuna kware wa a mulki da kuma wadanda suka nuna kwazo a bangaren yada ilimi. 

Ya ce sanata Rabi'u Kwankwaso, wanda Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) ya wakilta a wurin taron, ya samu kyautar ne saboda gudunmawar da ya bawa bangaren ilimi lokacin da yake gwamna a jihar Kano. 

Gumi ya kara da cewa gidauniyar ta karrama Wakala saboda kasancewar sa malamin addinin da ya shiga harkokin siyasa har ta kai ga ya rike matsayin mataimakin gwamna. A nasu bangaren, wadanda aka bawa kyaututtukan sun nuna jin dadinsu tare da mika godiya da gidauniyar marigayi Sheikh Gumi.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN