Legit Hausa
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya biya naia miliyan biyar
na tarar da aka ci wasu fursunoni a gidajen yari na urmawa da Goron Dutse duk a
cikin birnin Kano domin neman sakinsu. Da yake Magana a lokacin ziyarar da ya
kai cikin wannan wata na Ramadana, Sarkin ya bukaci fursunonin da su duba zaman
da suka yi a ggidan yari a matsayin nufi Allah sannan suyi amfani da hakan
wajen koyon darasi.
Ya shawarce su da suyi amfani da sauran ranakun da ya rage
na Ramadana wajen neman gafarar Allah da kuma neman yardarsa domin ya shiga
cikin lamarinsu. Ya kuma bukace su da su kasance masu kyawawan halayya domin
guje ma duk wani aiki da zai sa su sake komawa gidan yari.
Mukaddashin Shugaban gidajen yari na jihar Kano, Aliyu
Yahuza, ya bayyana ziyarar sarkin a matsayin abu da ke nuni ga cewa ya damu da
talakawansa. Ya kara da cewa gidajen yari sun jajirce sosai wajen horar da
fursunoni a fannin sana’o’i daban-daban.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI