Sarki Sanusi ya tsige Limamin wani Masallacin Juma'a a jihar Kano

Legit Hausa

Sarkin Kano ya cire babban limamin masallacin Juma'an Limawa -Sarki Sanusi ya tsige limamin ne sakamakon bijirema umarninsa kan sha'anin ganin watan sallar idi da ya yi har sau biyu -Limamin da aka ciren dai sunansa Salihu Muhammad wanda kuma yaki cewa komi a kan maganar yayin da 'yan jarida suka nemi jin ta bakinsa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido na biyu a ranar Juma’a ya bayar da umarnin tsige babban limamin masallacin Juma’an Limawa dake karamar hukumar Kumbotso a jihar, Malam Salihu Muhammad.

Tuni dakatar da wannan limami ya fara aiki ba tare da bata lokaci ba. Muhammad dai, ana zarginsa ne da sabawa umarnin Sarki a kan ganin watan sallar idi. Abinda wannan limamin ya aikata kuwa shi ne, bai ajiye azumi ranar da aka ga wata ba said a ya kara kwana daya bayan ya ga watan da idonsa sannan ya jagoranci ta shi sallar .Sanusi ya bayyana cewa ba yanzu limamin ya fara wannan dabi’a ba, ko a shekarar da ta gabata ya aikata irin wannan abu. Haka zalika, ya nuna cewa, tunda har dai limamin ya zama mai kunnen kashi ta hanyar maimaita laifin da aka gargadeshi a kai, to ya zama wajibi a sauya shi da wani daban. ‘Yan jarida sun tuntubi limamin da aka tsigen domin jin ta bakinsa amma abin ya gagara.

A wani labarin mai kama da wannan, mun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi Lamido na II ya yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda yake bada himma wurin yaki da talauci a kasar nan. Sarkin yayi wannan jawabin ne wurin wani taro na musamman da aka gudanar a jiharsa ta Kano, a karkashin ofishin babban ma'ajin gwamnatin tarraya.

DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post