Sai na tsugana sannan na ke ba Miji na abinci – Inji Jaaruma

Legit Hausa
Mun samu labari cewa Fitacciyar Malamar matan nan watau Hauwa Saidu Mohammed, wanda aka fi sani da Jaaruma ta fito tayi bayani game da yadda ake tafiyar da rayuwar aure har ya daure.
Jaaruma tayi wannan jawabi ne ta wani bidiyo da ta saki kwanan nan inda aka ga tana dukawa har kasa idan za ta ba Mai gidan ta abinci. Jaaruma tayi kaurin-suna wajen harkar rayuwar aure.
Wannan Baiwar Allah ta ke cewa: “Sunana Jaaruma, kuma ina girmama Miji na. Ina dukawa idan zan ba Miji na abinci.” Jaaruma ta kara da cewa: “Kyawun mace bai rike namiji a wajen diya mace.
Sai na tsugana sannan na ke ba Miji na abinci – Inji Jaaruma
Jaaruma ta na ba Mai gidan ta abinci har kasa a baki
“Ladabi da biyayya daga kowane bangare ne kurum ya ke rike aure.” Jaaruma ta bayyana duk wannan ne a bidiyon da ta fitar a lokacin da ta tsuguna har kas domin ta ba Mai gidan ta abinci.
Jaaruma ta maida martani ne ga ‘Yan matan da ke ganin kyawun su zai sa Namiji ya zauna da su komai runtsi. Jaaruma ta na ganin komai munin mace idan ta iya kwanciya, za ta rike Namiji.
Jaaruma, mai shekaru kusan 26 a Duniya, asalin ta Mutumiyar Garin Billiri ce daga jihar Gombe, wanda tayi fice wajen saida kayan mata da kuma bada shawarwarin yadda za a rike Mijin aure.
DAGA ISYAKU.COM
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN